Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Cross River, Bassey Otu, ya lashe zaben kananan hukumomi 12 daga cikin 15 izuwa yanzu da jami’an tattara sakamakon zaben kananan hukumomi suka bayyana a daren jiya.
Ya doke abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Sandy Onor, wanda ya yi nasara a kananan hukumomi uku, Kamar yadda Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Colombia Ta Dakatar Da Tsagaita Bude Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Masu Safarar Muggan Kwayoyi
Ana sa ran sakamako daga kananan hukumomi uku da suka rage, Obanliku, Boki da Akamkpa, yayin da aka dakatar da tattara sakamakon har zuwa ranar Litinin (yau).
Kananan hukumomi 12 da Bassey ya lashe sun hada da Yala, Calabar Municipal, Calabar ta Kudu, Obudu, Yakurr, Akpabuyo, Biase, Etung, Odukpani, Bakassi, Obubra da Abi.
Kananan hukumomi uku da dan takarar PDP ya lashe su ne Ikom, Ogoja da Bekwarra.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Jihar Cross River tana da kananan hukumomi 18.
Jami’in dake kula da tattara sakamakon zaben kananan hukumomi jihar a zaben Gwamna, Farfesa Teddy Adias ne ya jagoranci al’amura a hedikwatar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ke Calabar.
A wani labarin kuma,Bayan Abba Gida-Gida Ya Lashe Zabe, Gwamnatin Kano Ta Sanya Dokar Kulle
Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar ta-baci har zuwa faduwar rana, wanda ta ce da nufin kaucewa tabarbarewar doka da oda, sakamakon tashe-tashen hankula da suka taso a sakamakon tattara sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana hakan ne da safiyar Litinin din nan.