’Yan takarar jam’iyyar PRP a jihar Sokoto karkashin jagorancin Sa’idu Gumburawa, dan takarar gwamna a jam’iyyar sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda NAN ta ruwaito, Bashar Abubakar, mataimaki na musamman ga Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Lionel Messi Ya Kamo Maradona A Wani Tarihi
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan matakin nasa, Gumburawa ya ce ’yan takarar jam’iyyar PRP da za su koma jam’iyyar APC ne domin su bayar da gudunmawarsu wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.
“Mun yi la’akari da halin da mutanen jihar suka samu kansu a karkashin gwamnatin PDP,” in ji shi.
“Hakan ne ya sa muka yanke shawarar komawa jam’iyyar APC domin jihar ta dawo kan martabarta kamar lokacin gwamnatin tsohon gwamna Aliyu Wamakko.”
Baya ga Gumburawa, wasu da aka ce sun sauya sheka sun hada da ‘yan takarar sanata uku na jam’iyyar, Garzali Abdullahi, Bello Holai da Shehu Ibrahim na yankin Sokoto arewa, gabas da kudu, bi da bi.
“Haka zalika akwai ‘yan takarar majalisar wakilai 11 da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar 30,” in ji sanarwar.
Abubakar ya ce ’yan takarar jam’iyyar PRP da magoya bayansu sun samu tarba daga shugabannin jam’iyyar APC na jihar a ranar Juma’a.
Ya ruwaito Wamakko yana cewa ci gaban na daya daga cikin manyan nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a jihar gabanin zaben 2023.
“Na yi matukar farin ciki da karbar abokina kuma abokin aikina Gumburawa, wanda ke dawowa gida domin hada kai da mu domin ci gaban jihar Sakkwato,” inji Wamakko.
“A yau, ina so in tabbatar muku da cewa jam’iyyar APC da daukacin mambobinta za su ci gaba da hada kai da ku da magoya bayan ku don ba mu damar samun nasarar hadin gwiwa a zaben 2023.
A wani labari kuma, Gwamnan Arewa Ya Tsallake Rijiya da Baya Yayin da Babbar Mota Ta Murƙushe Motocinsa 2
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya tsallake rijiya da baya bayan da wata babbar mota ta murkushe wasu ayarin motocinsa biyu a ranar Asabar.
A cewar wani ganau, lamarin ya faru ne jim kadan bayan gwamnan da wasu kwamishinonin sa suka shiga wata bas kirar Mercedes a karshen wani daurin aure a masallacin Agga da ke unguwar Dougirei highbrow a Yola, babban birnin jihar