Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Filato, Dr Patrick Dakum a ranar Litinin ya taya zababben gwamnan jihar Mista Caleb Mutfwang murnar lashe zabe. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Dakum, wanda ya samu kuri’u 60,310 a zaben da aka kammala, ya taya Mutfwang na jam’iyyar PDP murna ta wayar tarho jim kadan bayan bayyana sakamakon karshe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe
Dan takarar jam’iyyar LP ya ce zai ci gaba da addu’a tare da marawa zababben gwamnan baya domin ci gaban jihar.
Sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta sanar tun farko, Mutfwang ya samu kuri’u 525, 299 inda ya kayar da abokin takararsa Dr Nentawe Yilwatda wanda ya samu kuri’u 481, 370.
A wani labarin kuma, An bai wa hammata iska tsakanin Sojoji da Yan sanda, Jami’ai biyu sun mutu
Akalla jami’an ‘yan sanda biyu ne aka tabbatar da mutuwar su a wata arangama tsakanin Yan sanda da jami’an sojin Najeriya a jihar Taraba.
Sojoji sun kutsa cikin hedikwatar ‘yan sandan domin ramuwar gayya kan zargin daba wa jami’insu wuka da ‘yan sanda suka yi tare da harbin ‘yan sanda kusan uku.