Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dokoki ta kasa ya rasa dansa Sadiq Kabiru Gaya.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Sadiq Gaya, lauyan hukumar kula da kadarorin Najeriya (AMCON) ya rasu ne a ranar Talata da yamma kuma aka binne shi a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Labari Cikin Hotuna: Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutane Da Muhallansu A Bauchi
Marigayin wanda ya kammala karatun shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar LL.M da ke kasar Wales , ya bar mata daya da ‘ya’ya biyu.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa Abba Anwar, Ganduje ya bayyana marigayin a matsayin mai tarbiyya, adali kuma mutumin al’umma.
Ya ce: “Duk da cewa muna son shi, amma Allah ya fi mu son sa. Namu shi ne addu’ar ya samu gafarar Allah da Aljannah.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan yana gidan Sanata Gaya da ke Abuja kuma ya jajanta masa da iyalansa kan wannam rashi.
A WANI LABARIN KUMA: Ana Zargin Wani Dalibi Ya Kashe Kansa A Hannun Hukumar Civil Defence
Wani matashi mai suna Musa David dan shekara ashirin da biyar a duniya a Sashen koyan harkokin kudi da aikin Banki da a Waziri Umaru Federal Polytechnic (WUFP) Birnin Kebbi ya kashe kansa.
David ya kashe kansa ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC a Birnin Kebbi.