Dan wasan kasar Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang ya yi ritaya daga buga kwallo, kamar yadda hukumar kwallon kafar kasar ta tabbatar.
Aubameyang na kungiyar Barcelona, wanda shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a Gabon da kwallaye 30 a wasanni 72, ya aika da wasikar ajiye takalmin nasa ga hukumar ranar Talata, inda ya tabbatar da hukuncin da ya yanke ke nan.
“Bayan shekaru 13 ina alfahari da wakilcin ƙasata, na sanar da cewa zan kawo karshen sana’ata ta duniya,” in ji ɗan kwallon mai shekara 32.
“Ina mika godiyata ga al’ummar Gabon da duk wadanda suka ba ni goyon baya a lokuta masu kyau da mara kyau.
“Zan kiyaye abubuwa masu kyau kamar ranar da na fara buga wasa… ko ranar da na dawo daga Najeriya da kyautar Ballon d’Or ta Afirka.
“Ina kuma so in gode wa dukkan kocina, ma’aikata da kuma ‘yan wasan da na samu a wannan aiki.”
Aubameyang an taba tabbatar da cewa yana dauke ya cutar Covid19 a Bara, kafin gasar cin kofin Afrika ta bana a watan Janairu sannan kuma ya fice daga wasan bisa abin da hukumar ta ce yana da matsalar zuciya.