An saka dan wasan gaba na Leicester City Kelechi Iheanacho a cikin rukunin wasannin mako na Premier.
Dan wasa Iheanacho ya zura kwallo daya kuma ya taimaka wajen cin kwallo biyu a wasan da Leicester City ta doke Aston Villa da ci 4-2 a ranar Asabar din da ta gabata.
KU KARANTA: EFCC Ta Kama Wani Manajan Banki Kan Boye Sabbin Kudin Naira
Wannan dai Ita ce kwallo ta biyu da dan wasan mai shekaru 26 ya ci a wasanni 15 da ya buga wa Foxes a wannan kakar.
Wannan ne karon farko da za a saka shi a cikin Tawagar da ta zo a mafi kyawun mako a wannan kakar.
An kuma zabi Iheanacho a matsayin gwarzon dan wasan bayan wasan.
Kazalika Shine dan wasan Leicester City daya tilo da aka zaba a zaben.
A wani labarin kuma: Kotu Ta Sake Bayar Da Umarnin Garkame Shugaban EFCC
Kotu ta sake bayar da umarnin kamo shugaban hukumar EFCC tare da garkame shi a gidan gyaran hali na Kuje.
Kotun tuni ta baiwa babban sifeton yan sanda umarnin kamo shugaban EFCC din, tare da tsare shi tsawon kwanaki 14.