Dan Wasan Fim na Nollywood ya kammala Digirinsa ta Biyu
Shahararren mak shirin film din Najeriyan Fim wanda ake Kira da Mike Ezuruonye ya kammala Digirinsa ta biyu daga babbar Jami’a dake kasar Benin.
KARANTA:- Dole Mu Kori APC Daga Najeriya Idan Munason Mudaina Shan Wahala, Wike
Dan wasan dai ya bayyana hakane ta kafar sada zumunta dake Instagram a ranar Juma’a.
Yayin da yake bayyana haka a wani faifan bidiyo da ya saki yace da masoyansa daga yanzu su rinka kiransa a matsayin babban Likita daga yanzu, sannan yana nuna matukar godiyarsa ga masoyansa.
Yace wannan ya samune ta irin soyayyar da kuke nuna mani da Kuma Mutanen kirki kewaye dani, yace Babban Likita Machael Ezuruonye yana sanku.
Shahararren dan wasan ya kammala Digirinsa a fannin Rubuce-rubuce da Zane-zane.
Comments 1