Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya caccaki ‘yan siyasar Najeriya kan ci gaba da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ke yi.
Musa ya caccaki ‘yan siyasar a shafin sa na Instagram ranar Talata, ya kuma tambayi yadda suka ji a lokacin da suka fita kasar waje domin ziyartar makarantun ‘ya’yansu, yayin da daliban Najeriya ke makale a gida.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/2023-tinubu-shettima-zasu-cika-tarihin-buhari-tare-da-ceto-najeriya-daga-illar-yakin-rasha-da-ukraine-bagudu/
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa yajin aikin ASUU ya shiga wata na biyar,inda ba aga wani cigaba ba wajen kawo karshen sa saboda har yanzu malaman ba su sauya wasu bukatunsu ga gwamnatin tarayya ba.
A ranar litinin da ta gabata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kai ziyara garin Daura na jihar Katsina domin gudanar da bukukuwan Sallah, ya koka da yajin aikin yana mai cewa ya isa a ajiye dalibai a gida.
Sai dai dan wasan da ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013, ya yi kakkausar suka ga matasan da ke rera wakar yabo ga ‘yan siyasa duk da cewa ba su yi karatu ba saboda yajin aikin.
“Zuwa ga masu rike da mukaman siyasar mu wadanda ‘ya’yansu ke karatu a kasashen waje. Yaya kuke ji kuna ziyartar yaranku a kasashen waje, kuna daukar hotuna a makarantunsu kuna bugawa ta yanar gizo yayin da ASUU ke yajin aiki?
“Ku nuna mini wani shugaban oyibo wanda yaronsa yana makaranta a Najeriya. Shin me zaku taba?
“Kuma idan kun dawo matasan Najeriya za su taru su yi wa una wakar yabo,” Musa ya rubuta.