Wani mai yi wa kasa hidima (NYSC) ya mutu sakamakon wani harsashi da ya sameshi yayin wata artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Jami’an tsaron sun yi arangama da ‘yan bindigar ne a lokacin da suke kokarin tsallakawa babbar hanya a kauyen Kasarami da misalin karfe 8 na yammacin ranar Juma’a.
Daly trust ta ruwaito cewa harsashin ya Sami marigayin wanda ke aiki a Abuja ne yayin da yake kan wata motar haya da ta taso daga Abuja zuwa Kaduna.
Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar da bai so a bayyana sunansa ba saboda ba shi da izinin yin magana ya ce an kashe ‘yan bindiga kusan bakwai a yayin musayar wuta.
“Wanda abin ya rutsa da shi, harsashin ne ya kwace ya sameshi, saboda an yi mumunar artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigar da suka yi kokarin tsallaka babban titin kauyen Kasarami wanda hanya ce da suke amfani da ita. Amma jami’an tsaron da suka hada da sojoji a Rijana sun kashe kusan bakwai daga cikinsu tare da kwato babura,” inji shi.
Ya ce an garzaya da matashin asibitin Saint Gerald amma likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya ziyarci gidan iyalan mamacin da ke kan titin Gero, Tudun Nupawa a cikin birnin Kaduna inda wani makwabcinsa wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa marigayin mai suna Malam Aliyu ya mutum
An yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sai dai ba’a samu hi ta bakin Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba, ASP Jalige Mohammed,