An samu barkewar Harbe-harbe tsakanin dakarun Afghanistan da na kan iyakar Pakistan a ranar Litinin bayan da hukumomin Taliban suka rufe hanyar shigar kasar, duk da yadda take fama da tarin masu son shiga kasar ta wannan hanyar iyaka.
Dangantaka tsakanin kasashen ta kasance cikin wani hali, tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace birnin Kabul a watan Agustan 2021, inda Islamabad ta zargi makwabciyarta da baiwa kungiyoyin da ke dauke da makamai da suka kai hare-hare a kasarta goyon baya.
KU KARANTA: APC Ta Dakatar Da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa a Yankin Arewa Maso Gabas
An yi ta samun tashe-tashen hankula akai-akai a kan iyakar da galibin tsaunuka ke raba kasashen wanda babu wata gwamnatin Afghanistan da ta taba amincewa da su gami da harbe-harbe na lokaci-lokaci da kuma rufewa.
Wani jami’in Pakistan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa an rufe mashigar Torkham da ke tsakanin Kabul da Islamabad da yammacin ranar Lahadi bayan da jami’an Pakistan suka mayar da wani matafiyi da ke tare da wani mara lafiya.
A ranar Litinin da karfe 7:30 na safe agogon Afghanistan (0300 GMT) an yi arangama a lokacin da sojojin Pakistan a inda suka yi luguden wuta kan sojojin Afghanistan, in ji wani jami’in Afghanistan Harfat Muhajir.
Mohammad Sediq Khalid, kwamishinan Torkham a bangaren Afganistan ya ce An rufe iyakar ne bisa umarnin jami’an Kabul bayan korafin cewa Pakistan ba ta cika alkawuran da ta dauka ba.
Wata majiyar tsaron kan iyakar Pakistan ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, takaddamar da aka samu kan matafiyin ta samo asali ne daga wata sabuwar bukata ta ma’aikatan jinya na dauke da wasu takardu.
Gwamnati ba ta amsa bukatar kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ba na fayyace sabbin dokokin.
Matsala ta kan iyaka a Torkham mai tazarar kilomita 177 (mil 110) daga babban birnin kowace kasa wata muhimmiyar hanyar kasuwanci ce, inda Afghanistan ke fitar da manyan motocin dakon kwal tare da karbar abinci da sauran kayayyaki daga Pakistan.
Kasashen biyu dai na cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki, inda kasar Afganistan ta yi fama da tabarbarewar tattalin arziki bayan kawo karshen mamayar da Amurka ke marawa baya, sannan Pakistan ta gurgunta sakamakon koma bayan gida da kuma matsalar musayar kudaden waje da ta kai ga gaci.
A wani labarin kuma: Gangamin Jam’iyyar APC: LASTMA Ta Bada Shawarar Wasu Hanyoyi Da Za A Bi
Gwamnatin jihar Legas ta samar da wasu hanyoyi gabanin babban taron gangamin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da za a yi ranar Talata a jihar.
A wata sanarwa da babban Manajan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, Bolaji Areagba, ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, gwamnatin ta ce hanyoyin da za a bi za su rage wahalhalu a lokacin tafiye-tafiye kafin da kuma lokacin taron.