Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
Da alama dai haryanzu akwai takun saka a tsakanin Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, da kuma wasu masu gudanar da harkokin sana’ar su a cikin masana’antar, wanda a ke ganin kamar abin yalafa a dan tsakanin nan, sakamakon tsayawar da harkar fim din ta yi, saboda rashin kasuwar fina-finan.
To Amma wani sako da Darakta kuma jarumi Falalu Dorayi ya wallafa a shafin sa na Facebook, wanda wakilin Jaridar Dimokuradiyya ya yi nazari a kan sa, ya nuna haryanzu akwai sauran Rina a kaba
A cikin sakon da Falalu Dorayin ya wallafa ya fara da cewar “Na dauka Magariba ta yi, gari ya kusa wayewa. Ni ban ga in da dokar Hukumar ta ce, inda mutum baya tare da kai, in an kawo fim a cire sunan sa ba”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta kama masu Garkuwa da mutane 14
” Ni na dauka wannan kama karya tun a lokacin Rabo ta wuce. Sun bi ka sun yi rajista da kai, Sun zuba kudi sun yi fim sun kawo maka, ka cire sunan Darakta har fim guda uku”
” Wai ina hankalin mu ya ke, in muna Zalunci, ko dauka mu ke babu ranar sauka? Gaskiya cire sunan Sunusi Oscar 442 da sauya sunan wani karya doka ne, da tauye masa hakkin sa na dan kasa”
“Gaskiya Sunusi Oscar kana da damar ka kai Kara Kotu, kuma ina da yakini za ka yi nasara”
“An kafa dokar Hukumar tace fina-finai ne, domin ta kare addini da al’adar mutanen Kano, da Gwamnati, da kuma masu gudanar da harkokin sana’ar su a masana’antar” inji shi.
To Amma me ya sa a ke cin Kare ba babbaka?
Masu harkar fim dai sun dade su na takun saka da Shugaban Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Malam Ismaila Na’abba Afakallahu, a kan irin wannan baton, wanda a lokatu da dama a baya aka gurfanar da wasu a gaban Kotu, tare da tura su gidan Gyaran hali na tsawon kwanaki.
Sai dai kafin mu hada wannan labarin mun yi ta kiran Shugaban Hukumar tace fina-finai Malam Ismaila Na’abba Afakallahu, don jin ta bakin sa, amma bai daga wayar mu ba, da zarar hali ya yi nan gaba mun ji ta bakin na sa, za mu kawo muku rahoto akan hakan.