Dangantaka tsakanin kasar Chana da Amurka na kara tsami bayan da Chana ta sanar da soke lasisin ofishin Jakadancin Amurka dake Chengdu inda ta bukaci rufe shi kamar yadda Amurka ta rufe mata nata a Houston a farkon wannan makon.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Chana ta fitar ta ce; wannan halastaccen ramako ne kan irin abin da Amurka ta yi duk da yake ba haka Chana ke bukatar ganin dangantakar kasashen biyu ke gudana ba.
Shi dai wannan ofishi na Chengdu an bude shi ne a shekara 1985 kuma yana dauke da ma’aikata kusan 200.
Bayan da Amurka ta sanar da matakin ta ranar Laraba da ta gabata, ma’aikatar harkokin wajen Chana, ta bakin kakakinta Wang Wenbin ta ce ko shakka babu ma’aikatar za ta dakatar da harkokinta sai dai akwai bukatar Amurka ta sake tunani kan matakin wanda zai shafi huldar diflomasiyyar kasashen biyu kamar yadda rahoton gidan Rediyon Faransa ya tabbatar.