Majalisar Dinkin Duniya ta nada Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote da kuma shugaban Bankin raya nahiyar Afirka, Mista Akinwunmi Adesina, da za su jagoranci yaki da abinci maras gina jiki a duniya kuma za su kasance daga cikin shugabanni ashirin da bakwai da za su yi yaki da rashin abinci mai gina jiki a duniya.
Nadin shugabannin Babban Sakataren Majalisar Mista Antonio Guterres ne ya amince da hakan, inda za su yi aiki tare da kungiyar fadada samar da abinci mai gina jiki a daukacin fadin duniya.
A cikin takarda da kungiyar SUN ta fitar, ta ce shugabannin sun hadu ranar Talatar da ta wuce, domin daukar matakan da kungiyar tasa a gaba wato kashi na uku da ake sa ran fara aiwatar da shi a shekarar 2021 zuwa 2025. Bugu da kari, shugabnnin za su sake haduwa domin tsara nasarorin da kungiyar take son cimma a taron da za su gudanar a birnin Tokyo dake Japan a shekara mai zuwa.