Gidauniyar Dangote ta samar da wata cibiyar gwajin cutar corona ta tafi-da-gidanka a jihar Kano wadda za ta iya yi wa mutum 400 gwaji a rana.
A jiya Lahadi dai ne aka mika wannan cibiyar da sauran kayayyakin ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a asibitin Muhammadu Buhari da ke Giginyu bayan kaddamar da ita.
Wannan kari ne kan wurin killace masu dauke da cutar korona mai gado 600 da mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka ya bai wa jihar tasa.