Gidauniyar Attajiri Alhaji Aliko Dangote mai suna Aliko Dangote Foundation (ADF), ta kaddamar da wata katafariyar cibiyar gwajin cutar korona a Jihar Kano ranar Lahadi.
Cibiyar wadda za ta fara da gwajin samfuri 400, ana sa ran za ta koma gwada samfuri 1,000 nan da ranar 10 ga watan Mayu a kowacce rana.
Tuni kamfanin 54Gene ya kafa irin wannan cibiya a jihohin Legas da Ogun, kuma shi ne ya kafa ta Kano.
An kafa ta ne a cikin asibitin Muhammadu Buhari da ke birnin na Kano, inda da ma ake da cibiyar gwajin.
Aliko Dangote ya ce wannan yunkuri ne na taimaka wa gwamnati wurin yaki da cutar a Kano, inda zuwa yanzu ta halaka mutum takwas, a cewar gwamnatin jihar.
Kazalika, gidauniyar ADF tana kokarin mayar da asibitin kula da masu yoyon fitsari na Abubakar Imam cibiyar killace masu cutar korona mai cin gado 150.
Da take bayyana irin ayyukan gidauniyar, Shugabar ADF Zouera Youssoufou ta ce suna kuma taimaka wa tawagar kai daukin gaggawa wurin gano masu dauke da cutar a cikin al’umma.
“ADF za ta danka wa tawagar kai daukin gaggawa ta Kano (RRT) motar daukar marasa lafiya 10 – hudu nan take, shida kuma nan gaba – da kayan kariya guda biyu domin samun sauki wurin daukar marasa lafiya,” in ji ta.
Aliko Dangote ya ce: “Kwamitin yaki da cutar korona (CACOVID) yana gina cibiyar killacewa a filin wasa na Sani Abacha, za mu fadada ta da gado 150 a asibitin Abubakar Imam. Cibiyoyin biyu za su fara aiki da zarar tawagar kwararru sun tantance ta.”
Daga Bbc Hausa