Farashin man fetur ya sake rikitowa zuwa kasa da kusan kashi 20 a safiyar ranar Litinin musamman a kasuwannin yankin Asiya, inda aka sayar da ganga daya a kan Dala 15, farashin mafi kankanta a cikin shekaru fiye da 20 a tarihi kamar yadda RFI Hausa suka tabbatar.
Faduwar farashin ta samo asali ne sakamakon rashin mabukata wannan makamashi a mafi yawan kasashen Asiya, inda kamfanoni da masana’antu suka jima a rufe sakamakon annobar COVID-19.
Wannan na zuwa ne duk da cewa, kasashen duniya masu arzikin man fetur sun cimma matsayar rage man da suke hakowa da kusan ganga miliyan 10 a kowacce rana, matakin da suka dauka da zummar farfado da darajar hajar.