Darajar Naira ya kara raguwa da kashi 1 kan dalar Amurka a kasuwar canji ta bayan fage, inda a yanzu dalar daya ke daidai da naira 480.
A kusan makwanni biyu da suka gabata dai darajar nairar ta tsaya ne kan 475 kan dala guda kafin samun koma bayan a ranar Talata.
A gefe guda kuma wasu na ganin bukatar dalar Amurkan da za ta karu la’akari da sake bude iyakokinta na sama ga jiragen saman kasa da kasa da Nijeriya za ta yi a ranar 29 ga watan Agustan da muke, zai kara takura darajar naira da bankin kasar ya ragewa karfi har sau biyu a baya.