By Uzairu Lawan Rigasa
Wasu Yan bindiga da ba’asan ko su waye ba, sun kai hari Cibiyar gyaran hali na Abolongo dake garin Oyo na jihar Oyo, ind a suka yi sanadiyar tserewar Daruruwan fursunoni a gidan yarin a yammacin jiya Juma’a.
Mai magana da yawun hukumar a jihar, Olanrewaju Anjorin, ya tabbatar wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya hakan a safiyar yau Asabar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an saki dukkan fursunonin da ke gidan yarin yayin harin.
Wani mazaunin Oyo, wanda ya sanarwa da majiyar jaridar Dimokuradiyya game da wannan lamari a safiyar yau Asabar, yace, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren jiya Juma’a.
Majiyarmu ta ce, an yi amfani da wani Abu Mai fashewar kafin shiga gidan yarin yayin da ma’aikatan da ke dauke da makamai a gidan yarin suka tsere don cton rayuwar su.
Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho, kakakin Hukumar NCoS a jihar ya ce: “Ee. An tabbatar da cewa a zahiri harin ya faru.
“Kuma a yanzu haka, Konturolan Hukumar Kula da Gidaje ta Nigeria, da sauran manyan hafsoshi suna tantance halin da ake ciki”
“Amma, zan iya tabbatar muku da cewa, lamarin ya faru a zahiri” inji shi.