Gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wani kwamiti da zai raba kayan agaji don rage radadin matsin tattalin arziki da mutane ke fuskanta saboda matakan da aka dauka a baya-bayan nan don dakile ayyukan ‘yan bindiga a jihar kamar yadda Rahotanni suka tabbatar.
Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce ta lura da wahalar da mutane ke fuskanta sakamakon tsauraran matakan da aka dauka don kawo karshen hare-hare da garkuwa da mutane da kashe-kashen mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Don haka ne ta ga ya dace ta samar da abubuwan amfani na yau da kullum ga mutane musamman na karkara don saukaka masu.
Gwamnatin ta bukaci kwamitin ya yi rabon kayan agajin cikin tsoron Allah tare da tabbatar da adalci wajen yin kason.
An bukaci kwamitin ya hada kai da manyan masu ruwa da tsaki ba tare da an duba bambancin siyasa ba, wajen gudanar da rabon.
Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Iabarai Ibrahim Magaji Dosara, ta yi godiya ga al’umar jihar Zamafara bisa goyon bayan da ta bai wa gwamnati a kokarinta na tabbatar da tsaro a jihar ta Zamfara.