Gamayyar ƙungiyar dattawan yankin Arewa maso gabas mai fafutukar kawo zaman lafiya da ci gaba ta yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta sallamar manyan hafsoshin tsaro.
Gamayyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Zanna Goni, ta kuma koka kan abinda ta kira taɓarɓarewar harkokin tsaro a Najeriya.
A cewarsu, “Muna sake jaddada buƙatar zuba sabbin hannuwa da za su zo da sabbin manufofi waɗanda za su kai ga sauya fasalin tsaron ƙasa.
“Mun fahimci yadda lamura suka kai matuƙa wajen taɓarɓarewa ƙarƙashin waɗannan manyan hafososhin.
“Babu ko tantama yanzu kusan komai ya dagule a ilahirin ƙasa: kashe-kashen al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba daga ’yan bindiga, ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa yanzu sun zama ruwan dare.
“Hakan ya yi sanadiyyar jefa mutane cikin halin zaman ɗar-ɗar da rashin tabbas.
“Muna kira ga shugaba Buhari da ya saurari koke-koken mafi yawan ’yan Najeriya ta hanyar sauya fasalin tsaron ƙasa domin inganta harkar.
“A matsayinmu na dattawa, ba zai yiwu mu yi shiru ba alhali lamarin na ci wa ’yan Najeriya tuwo a ƙwarya.
“Har yanzu mun kasa fahimtar dalilin shugaban ƙasa na ci gaba da aiki da waɗannan manyan hafososhi duk da kiraye-kirayen da ake masa na sallamar su daga kusan kowane ɓangare.
“Muna tunatar da mai girma shugaban ƙasa cewa ’yan ƙasa sun gaji da gafara sa a harkar tsaro amma har yanzu ba su ga ƙaho ba; suna buƙatar gani a ƙasa,” inji dattawan.
An dai jima ana kira ga shugaba Buhari da ya sallami manyan hafsoshin ko za a samu sa’ida kan matsalar tsaron da ke ƙara ta’azzara kusan a kullum amma shugaban bai sauya su ba.
Hatta ajalisar tarayya sai da ta buƙaci shugaban da ya yi hakan, amma ya ƙi.