Yayin da ake ci gaba da bukukuwar ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya, dattawan siyasa a kasar na cewa tsarin mulkin na Dimokuraɗiyya bai yi wa Najeriya rana ba.
Hasalima suna ganin zuwan Dimokuraɗiyya Najeriya kara rikirkita mata lamari ya yi a madadin samun alfanu.
A hirarsa da jaridar Dimokuraɗiyya, wani dattijon siyasa a Najeriya da ya ga jiya ya ga yau Alhaji Mahmud Adamu Barden Bauchi Ƙerarriya, ya ce komawa tsarin mulkin Firaminista shi ya dace ga kasar.
Alhaji Mahmud Adamu ya bayyana cewa tun farko kasar nan shishshigi ne ya kaita ga aron wannan tsari daga Amurka, inda ya ce kwata-kwata mulkin Dimokuraɗiyya bai dace ma ga nahiyar Afirka ba.
Bugu fa kari dattijon ya ce tarbiyya da aka sauya al’umma daga tsarin da aka sansu tun farko ita ce ta wargaza lissafin harkokin Dimokuraɗiyyar Najeriya, lamarin da ya sa yanzu haka aka dora al’umma a kan turbar bani-bani.
Hanya daya ta gyara tabarbarewar kasar nan kamar yadda Barden Bauchi Ƙerarriya ke cewa ita ce, maido da kasarnan ga tsarin mulkin Firaminista.
Ko da yake ya ce jahilci na da rawa da ya taka ga tsaikon da kasar nan ke samu, amma ya ce kauracewa zama yan amshin shatan yan siyasa ka iya zama mafita ga wannan al’amari.
Da ya tabo ɓangaren sauya ranar ta Dimokuraɗiyya kuwa daga 29 ga watan Mayu zuqa 12 ga watan Yuni da ake kira June 12, dattijon siyasar ya ce lallai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kyakkyawar dabara, don haka na iya zama silar ci gaban kasar nan a matsayin tsintsiya madaurin ki guda.
Haa zalika ya ce su ma yan jarida na da gagarumar rawar da za su iya takawa wajen hada kan kasar nan tare da baiwa al’umma damar morar romon Dimokuraɗiyya, ta hanyar wayar wa jama’a kai dangane da hakki da yancinsu.