By Abbas Yakubu yaura
Gwamnatin jihar Osun tace nan ba da jimawa ba za ta fitar da sunayen mutane 3,170 da suka yi nasara a jarabawar daukar malamai a jihar, wadanda suka samu adadin kashi 50 na maki zuwa sama.
Kwamishinan Ilimi na jihar Osun, Mista Folorunso Bamisayemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya rabawa manema labarai ranar Alhamis, a Osogbo.
A cewar Bamisayemi, mutane 3,170 da suka nemi aiki a cikin jimillar 11,068 da suka shiga aikin daukar ma’aikata sun samu kashi 50 cikin 100 na maki da sama da haka, kuma za a fitar da sunayensu, daga mako mai zuwa, a rukunin uku.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Ma’aikatar ilimi ta na sanar da jama’a, musamman masu neman aikin daukar malaman makaranta cewa an shirya jerin sunayen wadanda suka yi nasara da suka samu kashi 50 cikin 100 na sakamako da sama da haka a jarrabawar da kuma hirar kwarewa da aka yi dasu.
“Don tabbatar da dorewar albashi, za a dauki ma’aikatan ne a rukuni rukuni, saboda haka, daga cikin masu neman 3,170 za a fara zana jerin sunayen mutane 1000 da suka fi samun nasara a cikin darussa shida masu muhimmanci na Ingilishi, Lissafi, Biology, Chemistry, Physics da harkar Noma.
“Wannan jeri zai fito a cikin jama’a nan da mako mai zuwa, sannan kuma rukuni na gaba za su biyo baya, ”in ji sanarwar.