Gwamna David Umahi ya bayyana cewar Gwamnatin Jahar Ebonyi zata ɗauki a ƙalla Ma’aikata dubu 5,000 tare da tallafawa mutane 10,000 a faɗin Jahar.
Umahi, wanda ya bayyana haka a Abakaliki a lokacin da yake sanya hannu a kundin kasafin kudin Jahar, yana mai cewa Majalisar Dokokin Jahar a kowane lokaci a shirye take ga Tsare-tsaren shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya ta samu sabbin mutane 35 da suka da Covid-19 a Jahohi 5 da Abuja
Ya bayyana cewar Majalisar Dokokin ta san ayyukan da ake nufi da Majalisa.
Yace “duk wanda yake tunanin basu iya ba, yaje ya same su zaiga abunda ake gaya masa.
“Ƴan Majalisar a shirye suke domin cigaban Jahar a kowane lokaci ta hanyar sadaukarwa.
Umahi yace Gwamnatin Jahar zata tabbatar da kammala manyan ayyukan data ke yi a shekarar 2022.
Ayyukan sun ƙunshi, filin jirgin sama, da filin wasan ƙwallo, da gadoji da hanyoyi da sauran su.