Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin daliban da aka sace a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko dake garin Tegina na karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja ya rasu a hannun masu garkuwa da mutanen.
Idan za a iya tunawa dai kusan makonni biyu da suka gabata ne wasu yan bindiga suka kutsa makarantar Islamiyyar inda suka yi awun gaba da dalibai sama da 150.
Majiyoyi da dama sun ayyana cewa a jiya Lahadi ne aka tsinci gawar yaron, a wani wuri yan kilomita da makarantar da aka yi garkuwa da su.
Wani shaidar gani da ido ya ce bis aga dukan alamu yaron ya rasa ransa ne sakamakon firgici daga harbe harben yan bindigar suka yi.