Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce a yanzu galibin dazuzzukan kasar sun zamma maboyar ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da makami, ‘yan bindiga da masu aikata laifuka.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawar sirri da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja kan matsalar tsaro a jiharsa.
Ya bayyana kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu da cewa abin takaici ne, ya kuma yi kira ga shugaban kasa da ya taimakawa gwamnonin jihohi.
Ya kuma bukaci a kafa wani sansanin horas da sojoji a dajin da ke kan iyaka da jihohin Kano, Kaduna, Bauchi da Filato, domin duba ayyukan ‘yan ta’adda.
“Akwai kalubale a duk fadin kasar nan wadanda abin takaici ne, amma mun yi imanin cewa shugaban kasa yana yin iya kokarinsa tare da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile lamarin.
“Muna bukatar taimakon kusan kowa da kowa, musamman gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi. Mun lura cewa matsalar tsaro a yanzu, dajin mu ne manyan matsalolin saboda suna daukar ’yan bindiga, ‘yan ta’adda, da ‘yan fashi da makami kuma suna karbar wadanda suke da laifuja daban daban.
“A jihar Kano mun dauki wasu matakai. Muna da manyan dazuzzuka guda biyu, dajin Falgore, wanda ke kan iyaka da Kano, Kaduna da Bauchi, shi ma ba shi da nisa da Filato. A wannan dajin, mun kafa sansanin horar da sojoji tare da hadin gwiwar Sojoji,” inji shi.