Mataimakin Kwamishinan Ƴan sanda DCP Abba Kyari ya goge dukkanin rubuce-rubucen shi a shafin sa na Facebook, jim kaɗan bayan ya ɗora hotuna 462 daga bikin Maina Alƙali, ɗan gidan Shugaban Ƴan sanda na Ƙasa a Maiduguri.
Akwai wasu bayanai dake yawo cewa ya goge hotunan shi, bayan yayi wani rubutu daya wallafa wanda wasu gidajen jaridu suka buga Labarin.
Zuwan Kyari a bikin, shine na farko a watan, bayan ana sake yi masa bincike akan zargin da ake yi masa na alaƙa da damfara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na shiga Jam’iyyar PDP ne saboda rashin iya siyasa a Kano — Cewar Muhuyi Magaji
A cewar Kotu a Amurka a shekarar 2021, Hushpuppi wanda cikakken sunansa shine Ramon Abass, an zarge shi da cewa ya baiwa Abba kyari cin hanci domin ya kama Vincent abokin damfarar sa.
Hushpuppi an kama shi a Ƙasar daular Larabawa Dubai, bayan an zarge shi da damfari mutane Miliyan 1.9 da adadin kuɗin yakai Naira biliyan 168.
Ɗan Damfarar an zarge shi da baiwa Kyari kuɗade domin ya kulle abokin adawar sa bayan rashin jituwa akan Dala Miliyan $1.1 bayan ya damfari mutanen Qatar.
Kyari dai ya musanta batun karɓar kuɗaɗen daga hannun Hushpuppi, inda yace lafiyar sa ƙalau.