Direba ya saci motar Uwargidansa, ƴan awanni bayan ya fara aiki
A ranar Laraba ne wata kotun majistare da ke Ikeja ta tsare Samuel Harrison a gidan yari na Kirikiri bisa zargin satar motar Ubangidansa da wasu kayayyaki masu daraja.
Alkaliyar kotun, Misis O. O Fajana ta bayar da umarnin tsare wanda ake kara bayan ya amsa laifin hada baki da sata.
Fajana ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Satumba domin yanke hukunci, kamar yadda NAN ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: JAMB Ta Nemi Ikon Cin Gashin Kanta, Da Cire Ta Daga Kasafin Kudi Na Kasa
Mutumin mai shekaru 46 da haihuwa yana zaune ne a unguwar Ilaje da ke Ajah a Legas.
Mai gabatar da kara, Sufeto Funmilayo Akinleye ta shaida wa kotun cewa ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Yuli a Lekki, Legas.
Hakan ya saɓawa sashe na 287 da 411 na dokokin laifuka na jihar.
Dan sandan ya sanar da kotun cewa mai shigar da kara, Janet Essien ta dauki hayar Harrison a ranar da aka ambata.
Wanda ake tuhumar ya kai maigidansa wajen aski, a ranarsa ta farko da ya fara aiki ya jira a waje. Amma Essien ba ta same shi ba lokacin da ta fita daga baya.
Akinleye ta ce, “an same shi da wayoyi ƙirar Iphone guda biyu masu daraja, N600,000 da kwamfutar tafi-da-gidanka na apple daya, N550,000 suna cikin motar, jimlar Naira miliyan 8.1,” in ji Akinleye.
Mai gabatar da kara ya bayyana cewa an binciki motar kuma a karshe aka kama Harrison a Isolo.
A wani labarin kuma: 2023: Zaiyi Wahalar gaske a samu wanda zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a Zagayen Farko – Hunkuyi
Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaben 2023, ya lura cewa samun wanda zai lashe zaben shugaban kasa a fili bisa ka’idojin zabe na zaben farko na iya zama da wahala.
Ya kara da cewa, a zaben 2023 na gaskiya, gaskiya da adalci, babu wata jam’iyyar siyasa babba ko karama da za a yi watsi da ita domin duk wani abin mamaki zai iya faruwa.