By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi mai suna Haliru Aliyu mai shekaru 32 a duniya bisa laifin kitsa garkuwa da kansa kan kudi naira 500,000.
An kama Aliyu da Ahmed Ladan mai shekaru 42 bisa korafin da jami’an ‘yan sanda dake ofishin hukumar leken asiri ta jihar Gombe suka samu.
Wata sanarwa da wakilinmu ya samu ta hannun jami’ar hulda da jama’a na rundunar, Mary Malum, tace lamarin ya shafi hada baki, tsoratarwa, garkuwa da mutane da kuma karbar kudin fansa.
Malum tace, “Wanda ake tuhuma na farko, Haliru Aliyu ‘m’ na Tudun Wada dake unguwar Gombe, ya samu babur ne da kanwar sa ta ba shi ya hau bayan kasuwancinsa ya ruguje.
“Duk da haka, wanda ake zargin ya sayar da babur din a kan kudi Naira 250,000 ba tare da sanin mai shi ba.
“Lokacin da maigidan ya bukaci a ba shi babur din sa mai kafa uku ko kudinta, wanda ake zargin ya kasa kawo ko daya daga ciki. Saboda abin kunya, a cewarsa, a ranar 30 ga watan Disamba shekarar 2021, wanda ake zargin ya je gidan abokinsa, wanda ake tuhuma na biyu, Ahmed Ladan, inda suka hada baki da karya tare da yin garkuwa da wani mai suna Haliru Aliyu da niyyar ya karbi kudi agurin kanwarsa wata mai suna Zainab Aliyu ‘f’ mai shekara 42 wadanda suke wurin zama daya,akan kudi naira 500,000 domin ya dawo mata da kudin.”