Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira da ‘The United Global Resolve for Peace Organisation,’ ta nemi da a kwace kujerar Yakubu Dogara, wanda yake dan majalisar tarayya ne sakamakon komawarsa jam’iyyar APC.
Dogara ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya mika takardar ficewarsa daga jam’iyyar ga shugaban PDP dake gundumar Bogoro ‘C’dake karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi a ranar 24 ga watan Yulin 2020. Dogara ya ce ya fice daga jam’iyyar ne bisa ga karfa-karfa da ya ga ana yi a cikin jam’iyyar a jihar.
Sai dai kungiyar cikin takardar karar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/883/2020 ta hannun Lauyanta, Michael Okejimi & Co. Law Empire wanda majiyarmu ta samu kwafenta, ta nemi da kotu ta kori Dogara daga kujerarsa tare da ayyana kujerar a matsayin ba mai ita.
Har wala yau kungiyar ta nemi kotu da wanda aka shigar da kara na 4 da duk wani mutum ya daina kallon wanda aka shigar da kara na 1 a matsayin dan majalisar wakilai.
Mutum shida da aka shigar da kara sun hada da; (1)Tsohon Kakakin majalisa, Yakubu Dogara, (2) PDP (3) APC (4) Kakakin majalisar Tarayya (5), INEC (6) AGF.
Pelumi Olajengbesi, wani Lauya wanda ya goyi bayan shigar da wannan karar gaban kotu, ya ce akwai bukatar Dogara ya bar kujerar da yake a kai na dan majalisar tarayya.
Ya zuwa yanzu ba a sanya ranar da kotu za ta fara sauraren karar ba.