Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Keke Kyari ya sha alwashin kawo karshen Dogayen Layin da ake fuskanta yanzu haka a gidajen man ƙasar nan.
Kyari ya bayyana hakan a yau, yayin da ya bayyana gaban kwamitin wucin gadi na kula da matatun man fetur na majalisar wakilai ta tarayya.
Ya kuma ce akwai wadataccen mai yanzu haka a kasa, wanda zai taimaka wajen kawo biyawa kowa bukatarsa.
Ya kara da cewa yanzu haka akwai litar man Biliyan 2.8, wanda kuma zai ishi yan kasa, nan da zuwa kwanaki 47 ba tare da ya katse ba, ko kuma an shigo da shi daga waje.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar IPMAN ta sanar da cewa Dogayen Layuka da ake gani yanzu zasu ci gaba, kuma yan kasa su shirya.
Ya kuma alakanta layulan da akan samun a gidajen man da cewa saboda bikin sallah ne, da kuma ƙarewar hutun da aka yi ga ma’aikata da dalibai.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar IPMAN ta sanar da cewa Dogayen Layuka da ake gani yanzu zasu ci gaba, kuma yan kasa su shirya. Duba da cewa da yawa daga cikin mambobinta suna bin gwamnatin tarayya makudan kudi.