Ministar harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu, Naledi Pandor ta bayyana cewa; a dokokin kasar su bai ba da damar biyan diyyar barnar da aka yiwa ‘yan kasashen waje a kasar ba sakamakon hare-haren da aka kai wa baki ‘yan kasashen waje. Sai dai ta ce; kasar Afrika ta Kudu tana ci gaba da tattauna da hukumomin Nijeriya domin ganin an dawo da zaman lafiya. Inda ta tabbatar da cewa; kasar Afrika ta Kudu ta rufe ofishin Jakadancinta a Nijeriya na wani dan lokaci bisa fargabar kai musu hari sakamakon kashe ‘yan Nijeriya da ake yi a kasar Afrika, kamar yadda Ministar ta shaidawa kafar watsa labarai ta Reuters.
Ministar a taron tattalin arziki da ke gudana a birnin Cape Town na kasar, ta tabbatar da cewa za su ci gaba da tattaunawa domin ganin an dakile rikicin tsanar baki da ake yi a kasar.