Jami’an tsaro na NSCDC reshen jihar Ondo sun cafke matafiya mutum biyar wadanda suka ce sun karya dokar hana fita da gwamnatin jihar suka sanya.
Kwamandan NSCDC din na jihar, Philip Ayuba shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Kakakin hukumar na jihar Olufemi Omole ya rabawa manema labarai a ranar Talata a garin Akure.
Ayuba ya ce matafiya biyar din da aka cafke jami’ansu na NSCDC ne suka kama su a ranar Lahadi inda suka mika su zuwa ga kwamitin lura da dakile cutar Korona ta jihar.
Matafiyan a yayin bincikensu sun tabbatar da cewa daga garin Sakkwato suka fito inda suka yada zango a garin Ibadan na jihar Oyo.