Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, CP Hakeem O. Odumosu, ya shaida wa manema labarairanar Litinin cewa sun kama mutum 2,300 bisa laifuka masu alaka da kullen da jihar ta sa da manufar dakile cutar korona.
CP Hakeem ya ce tuni suka gurfanar da mutum 2,185 a gaban kuliya inda aka yanke musu hukunci daban-daban.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce sun kuma saki mutum 125 da ake zargi da karya dokoki wadanda suke da kananan shekaru.
Har wa yau, rundunar ‘yan sandan ta jihar Legas ta sha alwashin tabbatar da ‘yan jihar sun bi dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya da aka fara ranar 4 ga watan Mayu 2020, inda CP Hakeem ya ce sun dauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin mutane ba sa zirga-zirga tsakanin karfe 8:00 zuwa 6:00 na yamma.
Ya kara da cewa za su sanya kafar wando daya da duk mutumin da aka samu ya karya dokar sanya takunkumi.
-Bbc Hausa