A cikin jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yiwa ‘yan kasa a cikin daren Litinin dangane da cutar Koronabairos, shugaban ya ce; tafiye-tafiye tsakanin jiha zuwa wata jihar, dokar haramta zirga-zirgar za ta ci gaba da aiki har sai abin da hali ya yi, inji Buhari.
A karshe shugaban ya yabawa ‘yan Nijeriya, tare da ba su hakuri kan halin matsin da suka shiga, bisa bin umurnin dokokin da gwamnati ta kafa, hana fita domin dakile yaduwar annobar Korona da ta ratsa jihohin kasar 32 ciki harda Abuja.