Kwamitin Kar-ta-kwana kan annonar COVID19 na kasa karkashin Jagorancin Boss Mustapha ta kara tsawaita dokar kulle a Jihar Kano har na tsawon sati biyu.
Mustapha ya bada wannan sanarwa ne a yayim da yake bada karin haske game da cutar ga kwamitinsa.
Ya zuwa yanzu dai ana dakon sanarwa daga bakin gwamnatin Kano dangane da ranakun da mutane zasu ke fita domin samun sassaucin dokar. Jama’ar Kano na jiran sanarwar da gwamnatin zata bayar duba da ganin bikin Sallah karama na karatowa.