Gwamnatin tarayya ta sanar da kwaso mutane 102 ‘yan asalin Najeriya da dokar kulle ta ritsa dasu a kasar Masar sakamakon bullar annobar sarke numfashi ta Corona.
Hakan ya fito ne daga bakin Ministan harkokin kasashen waje Mista Geoffrey Onyeama, inda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.
Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta kwaso mutane daga kasashen Saudia da kuma kasar China.
https://dimokuradiyya.com.ng/covid19-kasar-indiya-ta-kwaso-mutane-312-daga-najeriya/
A yau kuma an sake kwaso mutane 102 daga kasar Masar, bayan da gwamnatin tarayyar ta tura mutane 260 ‘yan asalin kasar Indiya zuwa kasarsu.
Ministan ya bayyana cewa girjin Egypt shi ne jirgin da ya kwaso ‘yan asalin Najeriyar.
Yanzu haka ana san ran gwamnati zata killace su na tsawon sati biyu kamar yadda cibiyar dakile cututtuka ta kasa NCDC ta tanadar domin dakile annobar Corona.