Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta bayyana yadda bincikenta ya gano yadda masu ta’ammali da miyagun kwayoyi suka yi amfani da dokar kulle wajen ci gava da shan kwayoyi iri-iri.
NDLEA ta ce shan kwayoyi ba bisa ka’ida ba ya karu ta yadda masu shan miyagun kwayoyi suka yi ta harhadawa tare da kirkirar kayan maye iri-iri a tsawon lokacin kullen.
Shugaban hukumar, Muhammad Mustapha Abdallah, ya sanar da haka a ganawarsa da ‘yan jarida ta fasashar zamani yayin bikin zagayowar Ranar Yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da Safarar Dan Adam ta duniya ta shekarar 2020.