Yau Laraba 3 ga wani Yuni shekara ta 2020, ita ce rana ta farko da kasuwannin Kano aka bude su domin yin hada-hada, biyo bayan kulle gari da gwamnatin Kanon tayi saboda annobar Corona.
A shekaran jiya ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada umarnin sassauta dokar kullen da ake yi, sai dai gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace a Kano za a ci gaba da bude gari a iya ranakun Laraba, Juma’a da kuma ranar Lahadi.
A karon farko bayan bude kasuwannin mun samun rahotannin yadda aka yiwa kasuwar cikar-tsinke, inda ‘yan kasuwa da daidaikun mutane suka shiga yin saye da sayarwa domin ci gaba da kasuwancinsu kamar yadda aka saba.
Ga kadan daga cikin hotunan yadda kasuwar ta kasance a yau, hotunan mun samo su ne daga wajen Sani Maikatanga;





