A kallar mutane 269 ne suka iso gida Najeriya, wanda annobar Corona ta ritsa dasu a kasar Indiya biyo bayan dokar kulle da aka sa a kasar, kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito.
A safiyar Asabar din nan ne jirgin Air peace ya kwaso ‘yan asalin Najeriyar zuwa gida, mutane 103 ne suka sauka a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammed dake jihar Legas, sai kuma mutane 166 da suka sauka a filin tashn jirage na Nnamdi Azikwe dake babban birnin tarayya Abuja.
https://dimokuradiyya.com.ng/dokar-kulle-najeriya-ta-sake-kwaso-mutane-102-daga-kasar-masar/
Hakan ya fito daga bakin kungiyar ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje na shafinta na Twitter, inda kungiyar ta bayyana cewa wanda aka kwaso din zasu killace kansu kamar yadda doka ta tanadar.
“Dukkanin wanda aka kwaso din an killace su na tsawon satin biyu, kuma an gwada su inda aka tabbatar basa dauke da cutar, amma bayan awanni 72 cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC zata sake yi musu gwaji domin samun tabbacin basa dauke da cutar”. Kamar yadda kungiyar ta bayyana.