Shugaban kasa Muhammadu Buhari da makusantan sa na cikin rudani kan makomar masu rike da mukaman siyasa da za su iya yin murabus da yawa idan ya sanya hannu kan dokar zabe ta 2022 da majalisar dokokin kasar ta mika masa a ranar 31 ga watan Janairu.
Ana ganin tanadin da ya tilasta wa masu rike da mukaman siyasa masu son tsayawa takara a shekarar 2023 su yi murabus a matsayin cikas ga dokar zabe da ke gaban shugaban kasa a halin yanzu.
Amma wadannan wadanda aka nada, kamar yadda Daily Trust ta rawaito, ba sa son yin murabus saboda babu tabbacin za su dawo da mukamansu idan sun fadi zaben fidda gwani.
Aƙalla ministoci huɗu da wasu mutane da ke jagorantar ma’aikatu, sassan da hukumomi hakan ka iya shafar su Kai tsaye.
Jaridar ta ruwaito cewa shugaban kasar yana da wasu masu mukamai a siyasance a halin yanzu da ke rike da MDA da dama wadanda dokar da aka yi wa kwaskwarima za ta shafa idan aka sanya hannu kan dokar.
Wadanda aka nada a siyasance sun hada da ministoci 43, masu ba da shawara na musamman, manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman da shugabannin hukumomin gwamnati da ke rike da mukamai masu mahimmanci da ke da wuya a bayyana burinsu a fili.
A halin yanzu dai wasu daga cikin wadannan mukamai na siyasa ana yi musu kallon wadanda za su fafata a zaben shugaban kasa da na gwamna da na majalisar dattawa da na majalisar wakilai gabanin babban zabe na 2023.
Misali, sunayen ministocin sun hada da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu; Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da kuma Kwadago da Aiki, Chris Ngige; ana ganin suna daga cikin wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.
Comments 1