A safiyar Larabar da ta gabata ne wasu gungun ‘yan bindiga a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, suka kona wata mota da babura biyu domin tabbatar da bin umarnin zaman gida da haramtacciyar kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra (lPOB) ta bayar.
An ayyana zaman gidan a matsayin nuna jaje ga shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, wanda aka gabatar da shi gaban kotu a ranar Laraba, domin amsa tuhumar da hukumar DSS ta yi masa na cin amanar kasa da ta’addanci.
Wakilin Jaridar Daily Trust da ya zagaya babban birnin jihar ya lura cewa, bankuna da makarantu da wasu ‘yan kasuwa masu zaman kansu ba su bude wuararen kasuwancin su ba.
Maharan, wadanda ake zargin mambobin lPOB ne, sun zo ne a kan babura.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda Sun Kama Mutane 107 a Sansanin Soji na Bogi dake Legas
Rahotanni sun nuna cewa, Sun Kuma fara Kai Hare-haren ne a titin Hilltop kusa da tsohon ofishin hukumar DSS na jihar.
Wani ganau ya ce maharan sun kuma lakada wa masu motar da babura duka.
Sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan, DSP Loveth Odah, ta ce motar ta kama wuta ne saboda tsananin zafi ba sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai musu ba.
Ta kuma ce ba ta da masaniya kan abubuwan da suka faru ciki har da kona baburan.