Wasu mata gari sun cin na wa Wata babbar mota makare da kayan babur na milliyoyi nairori wuta, bisa kin bin dokar zama a gida da masu fafutukar kafa kasar Biafra suka sanya a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan, a kowace ranar Litinin.
Rahotanni na nuna cewa, lamarin ya afku ne da musalin karfe 6 na safiyar yau Litinin a garin Eluagu Obukpa na karamar hukumar Nsukka dake jihar Enugu.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Babbar Motar ta taso ne daga Nnewi na jihar Anambra, inda za ta nufi Ezike na jihar Enugu.
KARANTA WANNAN LABARIN: An sake kashe Mutane uku a karamar hukumar Bassa na Jihar Filato
Idan ba’a manta ba dai, Masu fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB, tun a watan Agustan shekarar nan suka ai’yana zaman gida a duk ranar Litinin a yankin Kudu maso Gabashin Nigeria, a yunkurin su na ganin an saki jagoran su Nnamdi Kanu, dake tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya.
Dokar zaman gidan da haramtacciyar kungiyar ta IPOB ta sanya ya fara aiki ne tun a ranar 9 ga watan Agustan da ta gabata, inda mazauna yankin ke koka wa kan yadda Shuwagabannin kabilar Igbo masu ne man ballewa daga Nigeria, suka kakaba musu wannan doka, inda Kuma suka bukaci da su janye wannan shawara da suka yanke.
Comments 1