Wani Bishop na addinin Kirista dake ƙarƙashin inuwar bishop-bishop na kasarnan ya bukaci majalisar dokokin tarayya da ta soke kotunan Shari’ar Muslunci a kasar.
Kazalika ya bukaci majalisar da ta soke dokar sashen nan na 10 da kuma 38 na kundin tsarin mulkin kasa da ta tanadar dokar addinin Musulunci a kasar.
Wannan batu nashi ma zuwa ne cikin wata takardar raba gardama da ya aike wa majalisar dangane da nazari kan kundin tsarin mulkin kasa.
Takardar wacce ta hadin gwiwa ce da shugaban CBCN Archbishop Augustine Akubeze da Sakatarensa Bishop Camilus Umoh suka sanya wa hannu, ta ce babu yadda za a yi a nuna wa Muslunci fifiko sannan a bar kiristanci duba da cewa suma suna da rinjaye.
Bisa ga wannan nazari nasu ne dai suka ce tilas ne a dakatar da kotunan musulunci a kasar ko kuma su ma a kirkiro musu da na kiristanci.