Babban Lauyan nan dake kare hakkin jama’a Mista Femi Falana ya ce babu makawa indai har ana so a kawar da cin hanci a kasarnan, to dole ne a rika hada sharia ana garkame manyan Lauyoyi da sauran manyan kwararu kan wata harka.
Femi Falana yana wannan batu ne yayin wani taro kan yaki da cin hanci da rashawa da wasu kungiyoyi suka shirya a birnin tarayya Abuja.
Ya ce matsawar ana zartar da hukunci ana tsallake kayin wadanda ke rajin yaki da cin hanci da rashawa, to lashakka matsalar cin hanci sai dai abunda za karu.
Ya kuma bukaci kungiyoyin kwararru a kasar nan da du rika taimakawa da bayana kan duk wani mamban su da aka samu da kashi a duwawu don zama izna ga yan baya.