DOLE NE AMURKA TA ƊANƊANI KUƊARTA NA KASHE JANAR QASEM SOLEIMANI~ Javad Zarif
Amurka ta hallaka kwamandan zaratan sojojin juyin-juya hali na Iran, Qasem Soleimani, a wani harin sama da sojojinta suka kai kan filin jirgin sama na Bagadaza, da ke can ƙasar Iraki.
Ma’aikatar tsaro ta Amurka, Pentagon ta sanar cewa Shugaba Trump ne da kansa ya bayar da umarnin kashe Janar Soleimani, wanda ta ce yana ta kokarin shirya yadda za a kai wa Amurkawa da ke Iraki zaune a Iraki hari a cewarta.
Hedikwatar tsaron ta kara da cewa harin wani gargadi ne, na duk wani hari da Iran za ta yi tunanin kai wa Amurka, inda bayan kisan aka ga Trump ya wallafa sakon wani katon hoton tutar Amurka a shafinsa na Twitter.
Wasu masana harkar tsaro a ƙasar ta Amurka sun ce Ya kamata Donald Trump ya yi takatsantsan’ domin kisan na Soleimani zai iya haifar da babban tarnaƙaƙi.
Wasu tarkace na cin wuta a wajen filin jirgin sama na Bagadaza inda aka kai harin
Janar din shi ne babban mai tsara dabaru na Iran a kan Iraki, inda ake kallonsa a matsayin babban mai tsara hare-hare da ayyukan kungiyoyin mayakan sa kai da Iran ke mara wa baya a Syria da Lebanon.
Kasashen Larabawa na daukarsa a matsayin wani shu’umi da ke iya bayyana a ko’ina kuma a ko da yaushe.
Ministan harkokin waje na Iran Javad Zarif ya bayyana kisan Janar Soleimani a matsayin wata tsokana mai hadarin gaske.
Ya ce wajibi ne Amurka ta dandana kudarta kan abin da ya kira kasassabarta.
Wani kakakin Iran ya ce babbar majalisar tsaron kasar za ta yi wani taro domin tattauna abin da ya kira, harin da ke zaman mugun laifi.
Farashin mai ya tashi:
Farashin mai a duniya ya yi tashin gwauron zabi bayan da aka tabbatar da kisan Janar Soleimani.
Farashin man samfurin Brent, ya karu da dala uku a kan ganga, inda ya kai kusan dala 70, lamarin da masu sharhi suka yi gargadin cewa za a iya samun matsalar fitar da mai daga yankin, idan zaman dar-dar ya karu.