Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bukaci ‘yan jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Gabas da su kara kaimi kafin zaben 2023.
Ya bayyana haka ne a Gombe ranar Asabar a wajen liyafar daurin auren Misbahu Yahaya dan Gwamna Inuwa Yahaya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Tsohon gwamnan na Legas ya tunatar da magoya bayan jam’iyyar APC cewa abokin takararsa Kashim Shettima ya fito daga yankin.
KARANTA ANAN: An Samu Sauƙin Kiran Waya Don Karbar Kudin Fansa – Pantami
Tinubu ya godewa ‘yan jam’iyyar da magoya bayansa kan abin da suke yi masa.
A nasa bangaren Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana yankin Arewa maso Gabas a matsayin shiyya ta biyu ga Tinubu bayan Kudu maso Yamma.
Shettima ya ce nan ba da dadewa ba za a fara gangamin siyasa, inda ya kara da cewa, Arewa-maso-Gabas yanki ne na APC don haka zasu yi duk mai yiwuwa domin nasarar jamiyyar.
A wani labarin kuma: Burtaniya Na Neman Iyalan Wasu Yan Najeriya Ruwa A Jallo Bayan Iyayensu Sun Mutu
Gwamnatin Birtaniya ta wallafa jerin sunayen ‘yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya mai tarin yawa a kasar Amma ba tare da an gano makusanta da za su gaji wannan dukiyar ba.
Jaridar BusinessDay da ake wallafawa a kasar, ta ce daga cikin dukiyoyin da mutanen suka mutu suka bari har da gidaje, wadanda a karkashin dokokin Birtaniya, matukar aka share tsawon shekaru 30 daga ranar da mai ita ya mutu amma ba a gano magadan mamancinsa ba, dukiyar za ta zama mallakin baitil-mali.