Babban Shehin Mallamin Addinin Islama nan Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci gwamnati da kada ta dauki ikirarin wadanda suka sace daliban jami’ar Greenfield a matsayin tatsuniya.
Gumi wanda ke wannan magana yayin zantawarsa da Jaridar Punch a Jiya Talata, ya ce tilas ya kamata Babban Bankin Najeriya CBN ya biya naira miliyan dari da masu garmuwar suka bukata don ceto daliban.
Kiran nashi na zuwa ne daidai lokacin da daya daga iyayen daliban yayi shelar cewa yan bindigar sun bukaci naira miliyan dari a gurin su gabannin su sake su.
Iyayen wanda ya bukaci a sakaye sunan shi, ya ce har yanzu yan bindigar suna kan bakar su ta cewa muddin ba a kawo wannan adadin kudin ba, to lallai zai aika daliban izuwa lahira.
Idan ba a manta ba dai a ranar ashirin ga watan Afirelun wannan shekara ne yan bindigar suka kutsa Jami’ar Greenfield dake Kaduna inda suka yi awun gaba da daliban da adadin su bai gaza 23 ba da wasu malaman su.
Kazalika a ranar Litinin din da ta gabata daya daga cikin jagororin yan bindigar, cikin wata tattaunawa da sashen haisa na muryar Amurka mai suna Kabiru Jalingo ya bukaci da a kai musu miliyan dari da babura guda goma kafin su saki daliban.
Cikin tattaunawar ya ce muddin gwamnatin Jihar Kaduna ko kuma Iyayen daliban suka yi kunne uwar shegu ba su kai kudin a ranar takata ba wato jiya kenan, to lallai za su yi asarar ya’yan su.