A kokarinsa na hada kan ‘ya ‘yan jam’iyar APC domin cimma nasara Sanata Uba sani Kaduna ya gana da ‘ya ‘yan jam’iyar a ranar asabar a karamar Hukumar Giwa dake jihar ta Kaduna Sanatan ne ya Sanar da Hakan a shafin sa na Facebook Yana Mai cewa na gana da ’ya’yan jam’iyyar APC a matakin unguwanni da kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Giwa karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na karamar Hukumar, Hon. Danladi Hudu da shugaban karamar hukumar, Hon. Abubakar Shehu Giwa. Taron ya ci gaba da kasancewa tare da masu ruwa da tsaki na babbar jam’iyyar tamu Mai daraja.
Na tunatar da masu ruwa da tsaki cewa, dole ne muradin babbar jam’iyyarmu ta Jihar Kaduna da Nijeriya ya kasance kan gaba a lissafinmu. Dole ne mu tabbatar da haɗin kai, haɗa kai da kuma mai da hankali don riƙe amanar jama’a.
Masu ruwa da tsaki sun sadaukar da kansu wajen ci gaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Giwa.
Sanata Uba sani dai babban jigon jam’iyar APC Mai mulki ne a jihar Kaduna.