Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsa ICPC ta ce dole ne ƙasashen duniya dake maido wa Najeriya kudaden sata da wasu marasa kishin lasa suka.je suka boye su rika haɗawa da ruwa.
A cewar hukumar idan ba ta haka aka yi ba, wadannan kasashen ba za su dadsara da adana miyagun kudaden yan Najeriya a kasar su ba.
Shugaban Hukumar Farfesa Bolaji Owasanoye wanda shine ya faɗi haka a birnin tarayya Abuja ya ce gwamnatin tarayya tana kan nazari kan hanyoyin da doka ta tanada don dakile mugun sace sace.
Farfesa Owasanoye ya kara da cewa yadda yan Afirka ke safarar kudade daga ƙasashen su zuqa turai tamkar na gidansu, ya zamo ruwan dare gama duniya, wanda kuma ya taimaka gaya wajen durkusar sa martabar nahiyar a idanun duniya kan abinda ya shafi hulda kudade na kasa da kasa.