Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi Mista Kingsley Fanwo ya Jaddada bukatar dake da akwai ta baiwa matasa masu jini a jika su mulki kasar nan a shekarar 2023.
Fanwo wanda ke magana kan irin jan-in-ja da ake yi kan ko wace shiya ce ya kamata ta mulki kasar a shekarar 2023 ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dubi Shiayar matasan da idon basira.
Ya ce “Ba za mu sake maganar dattawa ba kuma kan batun shugabancin Kasa a 2023, akwai wata shiya da ake kira da Shiyar Matasa, kama daga Arewa har kudu suna da wannan shiya da ya kamata a bata dama zuwa fadar Aso Rock.
Amma abin mamaki babu wani matashi da ya ziyarci fadar da sunan shugabanci tun da aka shiga Dimokuradiyya a 1999, don haka yanzu dama ce da ya kamata a basu.
Ya ce matsalolin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu na bukatar masu jini a jika ne muddin ana bukatar magance su.
Bugu da kari Kwamishinan ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi iya kokarinsa kuma yana ci gaba da yi don daidaita kasar.